Mun kama miyagun kwayoyi miliyan 12 da dubu dari hudu a jihohin Legas da Bauchi – NDLEA

0
146

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta kama miyagun kwayoyi milyan miliyan sha biyu da dubu dari hudu a Legas da Bauchi.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce kwayar Tramadol da jami’anta suka kama a filin jirgin sama na Legas ta kai ta naira biliyan 3.7.

Hukumar ta ce ta yi wannan kamun tare da hadin gwiwar jami’an kwastam inda suka gano kwayoyi har miliyan biyar da dubu dari da ashirin da biyu da dari tara (5, 122, 900).

Binciken wucin gadi ya nuna cewa an shigar da kwayoyin Nijeriya ne daga kasashen Pakistan da kuma Indiya inda wasu daga cikinsu kuma za a kai su birnin Freetown na Saliyo.

Kwayoyin na Jihar Bauchi da jami’an suka kama sun kai miliyan shida da dubu dari biyu da sittin da biyar da guda tamanin (6,265,080).

Wadanda ake zargi da safarar kwayoyin sun hada da Emmanuel Onyebuchi mai shekara 32 da Uche Iyida mai shekara 33 da Chinedu Ezeanyim mai shekara 32.

NDLEA ta ce an kama su ne a babbar hanyar zuwa Maiduguri a cikin garin Bauchi a ranar Laraba.

A sanarwar da hukumar ta NDLEA ta fitar a ranar Lahadi, ta ce ta kama gawurtaccen mutumin da ya shahara wurin safarar manyan miyagun kwayoyi zuwa Turai, musamman kasar Italiya.

“NDLEA ta kai samame dakin otel dinsa da ke yankin Okota da ke Legas a ranar Juma’a 21 ga watan Yuli a lokacin da yake shirya wani sabon dan aikensa ya hadiya kulli 93 na hodar ibilis da za a kai Italiya,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce Mista Charles Uwagbale ya dauki Uju Dominic mai shekara 32 aiki tun daga Italiya domin ya je Nijeriya ya hadiye kullin hodar ibilis 100 ya koma can Italiyar.

Hukumar ta ce an kama mutumin yana cikin shirin soma hadiye kwayoyin a ranar Juma’a da dare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here