Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke shirin kai wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar hari.
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon mataimakin shugaban kasar, Abdurrasheed Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, “Muna son sanar da ‘yan Najeriya cewa da misalin karfe 9:44 na dare. A ranar Lahadi, 23 ga Yuli, 2023, an kama wani mutum a kofar gidan Atiku Abubakar a Yola.
“Wani mutum ya shaidawa ‘yan sanda cewa sunansa Jubrila Mohammed, mai shekaru 29 kuma dan Boko Haram ne daga Damboa a jihar Borno.”
“Ya kuma shaida musu cewa shi da wasu abokan aikinsa guda uku, wadanda aka kama, sun shirya kai hari a wuraren da ke da alaka da Atiku Abubakar.
“An riga an mika wadanda ake zargin hudu ga sojoji.
Sanarwar ta kuma yaba wa rundunar ‘yan sandan kan wannan kokari tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da mai da hankali kan ayyukansu.