Kungiyar Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL), ta dauki matakin magance gurbacewar muhalli, don bunkasa noma a jihohin Arewacin Najeriya 19, da kuma FCT.
Dokta Abdulhamid Umar, Babban jami’in ACReSAL na kasa na ACReSAL, wani shiri na Bankin Duniya ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Jos, a wajen bude taron karawa juna sani ga ma’aikatan da ke gudanar da aikin.
Umar ya ce mahalarta 250 ne a Jos a kan sashin B na aikin, wanda ya shafi maido da amfanin noma da inganta rayuwar jama’a.
Ya ce matakin ya zama wajibi, tunda noma shi ne ginshikin jama’a, amma sauyin yanayi da sauran al’amuran dan Adam na yin illa.
“Don haka, muna nan don samun kyakkyawar fahimta da abun da Bangaren B, ke neman isarwa ga al’ummominmu da gidajenmu.
“Kididdiga ta nuna cewa yankin arewacin Najeriya ne koma baya sosai, sakamakon kalubalen sauyin yanayi.
“Haka ya kai yadda yanayin yankin arewacin Najeriya ya lalace da wargajewa, wanda hakan ya sa al’ummarmu suka yi hijira.
“Idan ka lissafta jahohi 11 na gaba a arewacin Najeriya, inda hamadar Sahara ta yi tsanani sosai, kamar Borno, Yobe, Jigawa, Katsina, Kano, Sokoto da Kebbi, da dai sauransu,” in ji Umar.
A cewarsa, ACReSAL tana Jos ne, saboda ayyukan hakar ma’adanai a tsawon shekarun da suka gabata sun lalata yanayin jihar Filato, har ta kai ga tafkuna sun zama tarkon mutuwa.
Mista Garba Gonkol, Ko’odinetan aiyuka na ACRESAL na jihar Filato, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa sakin kudaden takwararta da ta yi domin gudanar da aikin cikin sauki, wanda aka fara a karshen shekarar da ta gabata.
A cewar Gonkol, yanayin jihar na da kalubale da dama da suka hada da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa.
Ya kuma yi nuni da cewa, yawaitar ayyukan hakar ma’adinai da ba a kula da su ba da ake yi a sassa da dama na jihar, yana kara lalata yanayin kasar.
A nata bangaren, Dokta Joy Agene, Shugabar Task Team na aikin, ta bukaci jihohi da su samar da shawarwarin da za a iya aiwatar da su a cikin tsarin aikin.
Agene ya ce tuni jihohi bakwai suka gabatar da shawarwarin nasu, don haka yanzu za su iya tantancewa da ganin yadda za su fi dacewa da aikin da aka dora musu.
Ta bukaci jama’a da su mai da hankali wajen sanya tsarin cikin gida, da yadda za a aiwatar da shi.
Mista Manievel Sene, Jagoran Bangaren B, a cikin jawabinsa, ya bayyana cewa bangaren yana da B1 da B2, wadanda suka shafi karfafa al’umma da saka hannun jarin al’umma bi da bi.