DSS ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu

0
112

Gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) wanda aka dakatar, Godwin Emefiele, ya samu karasawa babban kutun da take zaune a tarayya da ke Legas kan gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ne suka gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa laifin da ake zargin sa da shi da misalin karfe 9:20 na safiyar ranar Talata.

Za a gurfanar da shi ne a gaban mai girma mai shari’a Nicholas Oweibo bisa tuhume-tuhume guda biyu da za a tuhume sa da su, mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.

A ranar 13 ga watan Yulin 2023 ne, gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da safarar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba kan gwamnan CBN da aka dakatar.

Gwamnatin Tarayya ce wacca ta zargi Emefiele da mallakar bindiga mai lamba JOJEFF MAGNUM 8371 ba tare da lasisin mallakarta ba.

Gwamnati ta ci gaba da cewa laifukan sun saba wa sashe na 4 na dokar mallakar bindiga karkashin sashe F28 da sashe na 27 (1b) na Dokokin Tarayya na 2004 da doka ta tanada.

An kuma tuhumi Emefiele da mallakar wasu harsasai ba tare da lasisinsu ba, wanda hakan ya saba wa sashe na 8 na dokar mallakar bindigogi F28 na tarayya na shekarar 2004 da kuma sashe na 27 (1) (b) (il) na wannan dokar.

Tun ranar 10 ga watan Yuni ne dai Emefiele ke hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) inda ake ci gaba da tsaurara bincike a kansa bayan da shugaba Tinubu yadakatar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here