Shugaban kasar Nijar na karkashin tsaro kan fargabar juyin mulki

0
126

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun rufe gida da ofishin shugaba Mohamed Bazoum.

Ƙasar da ke Afirka ta Yamma na daya daga kasashen da ke fama da rikce-rikice, inda ta fuskanci juyin mulki sau hudu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960 da kuma wasu yunkurin juyin mulki a baya-bayan nan.

Sai dai wata sanarwar jami’an tsaron kasar ta ce: “Shugaban yana lafiya, yana cikin koshin lafiya. Shi da iyalinsa suna cikin gida,” cewar majiyar.

An rufe hanyar shiga gida da ofishin Bazoum da ke fadar shugaban kasa da ke Yamai, duk da cewa babu wasu dakarun soji da aka jibge.

Juyin mulki na karshe a kasar ya faru ne a watan Fabrairun 2010, wanda ya hambarar da shugaba Mamadou Tandja na lokacin.

Duk da haka, an yi yunkurin wani juyin mulki a ranar 31 ga watan Maris, 2021, kwanaki biyu kacal kafin kaddamar da Bazoum a matsayin shugaban kasar.

An kama mutane da dama, ciki har da wani kaftin din sojin samar kasar mai suna Sani Gourouza.

An kama shi ne a makwabciyar kasar Benin sannan aka mika shi ga hukumomin Nijar.

A cewar wani jami’in Nijar, yunkurin juyin mulkin Bazoum na biyu ya faru ne a watan Maris din wannan shekara “a lokacin da shugaban ke kasar Turkiyya,” ko da yake hukumomi ba su yi wani bayani kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here