Doguwa ya samu shugabancin kwamitin man fetur na majalisa

0
69

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana sunayen wadanda za su jagoranci kwamitocin majalisar guda 134, a ranar Alhamis.

Daga cikin wadanda suka rabauta da shugabancin kwamitin akwai tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa da dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufa’i.

Kakakin dai ya bayyana kwamitocin ne guda 134 a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Alhassan Doguwa dai shi ne zai jagoranci kwamitin man fetur na majalisar, sai Bello El-Rufa’i da zai jagoranci kwamitin kula da bankuna.

Kazalika, dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji daga Jihar Kano shi ne zai jagoranci kwamitin harkokin waje, sai dan majalisar Bichi, shi ma daga Kano, Abubakar Kabir Abubakar, wanda ya jagoranci kwamitin ayyuka a majalisa ta tara, wanda yanzu zai jagoranci kwamitin kasafin kudi.

Shi kuwa tsohon Mataimakin Shugaban majalisar, Ahmed Idris Wase, ya rabauta da kwamiti yayin da Mukhtar Betara ya sami kwamitin Babban Binin Tarayya Abuja.

Dan majalisa Yusuf Adamu Gagdi ya samu kwamitin sojojin ruwa, sai Leke Abejide da zai ci gaba da rike mukaminsa na kwamitin hukumar Kwastam.

Bugu da kari, Kakakin ya ayyana sunan Kabiru Alhassan Rurum a matsayin shugaban kwamitin sufurin jiragen sama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here