Tajudden Abbas ya kaddamar da kwamitocin majalisar wakilai

0
112

Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai, ya bayyana sunayen ‘yan majalisar da za su jagoranci kwamitoci 134 a zauren majalisar.

Abbas ya bayyana sunayen shugabannin kwamitocin da mataimakansu a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Kundin tsarin mulkin Nigeria dai shi ne ya bayyana cewa yana daga cikin aikin yan majalisar su rika bibiyar aiyukan ɓangaren zartarwa ta hanyar kafa kwamitocin da zasu rika sanya idanu akan aiyukan ma’aikatu da Hukumomin gwamnati.

Ga wasu daga cikin sunayen yan majalisar da zasu shugabanci kwamitocin sun hada da James Faleke (finance); Muktar Betara (FCT); Akin Alabi (works); Bamidele Salami (Public account); Idris Wase ( hukumar federal character); Leke Abejide (custom); Jimi Benson (defense); Ahmed Satomi (national security) da Yusuf Gagdi (navy).

Sauran su ne Alhassan Doguwa ( petroleum resources upstream); Ikenga Ugochinyere ( petroleum resources doenstream); Sada Soli (weter resources), da Wole Oke (judiciary).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here