ECOWAS za ta yi taron gaggawa kan juyin mulkin Nijar a Abuja

0
133

Shugabanin kungiyar kasashe mambobin ECOWAS, zasu gudanar da wani taron gaggawa ranar Lahadi a game da juyin mulkin kasar Nijar a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.  

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin fadar shugaban kasa, Dele Alake yana mai cewa shugaban kungiyar ta ECOWAS kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar juye-juyen Mulki a yammacin Africa. 

Ta cikin Sanarwar, Shugaba Tinubu ya yi fatan wannan taron na su  zai samar da matsaya guda wadda zata bada damar mayar da jamhuriyar Nijar kan turbar Dimokradiyya. 

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris da sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Gutters sun bukaci Bola Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen dawo da martabar jamhuriyar Nijar ta hanyar kwatota daga hannun Sojoji a wata tattaunawa da su ta wayar tarho. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here