Wasu iyaye sun sayar da dansu sun sayi iPhone

0
99

Wasu ma’aurata a Yammacin Bengal da ke Indiya sun tabbatar da cewa sun sayar da dansu dan wata takwas don sayen wayar iPhone don su dinga yin bidiyo suna saka wa a soshiyal midiya.

Makwabtan ma’auratan a unguwar Panihati Gandhinagar sun fara dasa ayar tambaya bayan da suka ga matar da mijin sun sayi waya mai tsada tare da yin tafiye-tafiye a kewayen yankin Yammacin Bengal suna daukar bidiyoyi, yayin da aka daina ganin dan nasu.

Da ake tuhumarsu, mata da mijin sun amsa cewa sun sayar da dan ne ga wata mata a kauyen da ke kusa da nasu.

Ko a makon da ya wuce ma sai da miji da matar masu suna Jaydev da Sathi suka yi kokarin sayar da ‘yarsu ‘yar shekara bakwai, kamar yadda wani jami’i a yankin Tarak Guha ya fada.

Sakamakon amsa laifin da suka yi ne ya sa aka kama Sathi da matar da ta sayi dan, yayin da shi kuwa Jaydev ya tsere in da a yanzu ‘yan sanda ke nemansa.

Wata kafar watsa labarai a kasar News9Live ta tabbatar da cewa hukumomi sun samu nasarar kwato yaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here