Gwamna Radda zai ka kafa hukumar Zakka a Katsina

0
116

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce zai mikawa majalisar dokokin jihar kudirin kafa hukumar Zakka da Hubusi a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Malam Ibrahim Kaula ya fitar a Katsina ranar Litinin.

A cewar sanarwar, gwamnan ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin kaddamar da gidaje 400 a Dandagoro da ke karamar hukumar Batagarwa ta jihar.

“Hukumar za ta baiwa hukumar Zakka da Hubusi damar gudanar da ayyukan bayar da Zakka kamar yadda ya kamata,”

Radda ya yabawa shugaban gidauniyar Atta’awwun Islamic Foundation, Dr Ahmad Musa-Abdullahi, kan kaddamar da aikin samar da gidaje, ya kuma bada gudunmuwar naira miliyan biyar ga aikin.

Ya ce gwamnatin jihar da kananan hukumomi 34 za su bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 da daukar nauyin marayu da ‘yan gudun hijira a fadin jihar don rage musu radadi.

Sanarwar ta ruwaito Atta’awuni, ta tsara aikin ne a makarantu da cibiyar lafiya, wurin kula da kananan yara da koyar da sana’o’i.

Gwamnan ya yabawa al’ummar musulmin jihar da kuma na jamhuriyar Nijar da Ghana da Saudiya da kuma Amurka kan gudumawarsu da suka bayar a wannan aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here