Takunkumin da ECOWAS ta saka wa Nijar ya fara haifar da matsin rayuwa a kasar

0
163

Mazauna sassan Jamhuriyar Nijar sun fara kokawa game da tsadar rayuwa da suka shiga sakamakon rufe iyakokin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. 

Wasu ‘yan kasar musamman ‘yan kasuwa sun ƙara farashi kan kayayyakin masarufi, suna masu alaƙanta hakan da fara aiwatar da takunkuman da aka saka wa ƙasar sakamakon juyin mulkin na ranar Laraba. 

Lamarin na faruwa ne yayin da mambobin ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma suka fara aiwatar da takunkumin daina hulɗar kasuwanci da Nijar. 

Ƙasar Benin wadda maƙwabciyar Nijar ce ta ɓangaren arewaci ta rufe iyakarta.

Shugaba Mohamed Bazoum suka sanar da rufe iyakokin ƙasar ta ruwa da sama da kuma ƙasa ‘yan awanni bayan juyin mulkin. 

Baya ga takunkuman da ta saka wa Nijar ɗin, Ecowas ta kuma bai wa sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani mako ɗaya don su mayar da Bazoum kan mulki. 

Cikin matakan da ƙungiyar ta yi barazanar ɗauka har da na ƙarfin soja yayin taron da ta gudanar a Abuja ranar Lahadi. 

A ranar Juma’a ne Janar Tchiani ya bayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa bayan rundunar da yake jagoranta ta dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ta kifar da gwamnatin farar hula ta farko da ta karɓi mulki daga irinta a Nijar

Tuni kayan masarufi suka fara yin tashin gwauron-zabi a Yamai babban birnin ƙasar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here