An dakatar da manhajar TikTok a Senegal

0
146
TikTok
TikTok

An dakatar da dandalin sada zumunta na TikTok a Senegal a bisa zargin amfani dashi wajen tunzura rikici.

Ministan sadarwar ƙasar Moussa Bocar ya ce dandalin ya zamo shafin da masu son yaɗa kalaman ɓatanci da raba kan jama’a ke amfani da shi wajen cimma manufar su.

An ɗauki matakin dakatar da TikTok ɗin ne kwanaki bayan kama jagoran ƴan adawar ƙasar, Ousmane Sonko inda ake zargin shi da tunzura masu zanga-zanga da kuma wasu laifukan.

An kashe mutum uku a birnin Ziguinchor, garin da Ousmane Sonko ke jagoranta a matsayin magajin gari.

Hukumomi a ƙasar sun kuma katse sadarwar intanet na wucin-gadi a makonnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here