Juyin Mulki: Najeriya ta katsewa Nijar wutar lantarki

0
112
wutar lantarki

Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar da kuma sauran wasu manyan birane kamar Maraɗi da Zinder sun fara fuskantar katsewar wutar lantarki.

Mutane na samun wutar lantarki na ne na tsawon kimanin sa’a ɗaya a wani lokaci daga nan sai a ɗauke tsawon sa’a huɗu ko biyar ba tare da an sake kawowa ba.

Rahotanni sun nuna tsarin bayar da lantarki a babban birnin ƙasar ya koma zuwa bai wa wani ɓangare, a kuma kashe wa wani ɓangare a lokaci guda.

Kamfanin sarrafa lantarki na Nijar (Nigelec) ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon katsewar lantarkin da ake samu daga Najeriya. Ƙasar dai wadda shugabanta Bola Tinubu ke jagorantar ƙungiyar Ecowas na ɗaukar wannan mataki ne a wani ɓangare na takunkuman da ƙungiyar ƙasashen ta Afirka ta Yamma ta ƙaƙaba wa Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.

Gwamnatin Najeriya dai ba ta tabbatar da iƙirari ko musanta shi ba zuwa yanzu.

Sai dai, majiyoyi daga Abuja sun ce hukumomin ƙasar sun katse wasu layukan wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar, ba tare da yin cikakken bayani ba.

Najeriya, ita ce ƙasa mafi samar da lantarki ga Jamhuriyar Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here