Ƙasashen Yammacin Afrika sun amince da wani tsari na ɗaukar matakin soji kan Nijar, idan har sojojin da suka yi juyin mulki suka ƙi amincewa da sharaɗin dawo da hamɓarren shugaba, Mohamed Bazoum bisa karagar mulkin.
Tun da farko ECOWAS ta bai wa sojojin na jamhuriyar Nijar wa’adin ranar Lahadi su mayar da mulki ga farar hula.
Alamu na nuna cewa sojojin Ecowas sun ƙagu da su ƙaddamar da yaƙi a Nijar idan har hakan ya zama dole.
Yanzu haka dai, Najeriya ta rufe iyakokin ƙasar da Nijar, ta kuma yanke wutar da take bai wa Nijar din duk a lokaci guda, matakan sun haddasa tashin farashin kayan masarufi a ƙasar, hakan na nuna yadda matakan Ecowas ɗin za su haddasa wahalhalu ga ƴan ƙasar.
A ranar Alhamis wata tawaga ta kungiyar ta je Nijar, domin shiga tsakani sai dai ba ta samu damar ganawa da shugaban mulkin sojin ba, da ma hamɓararren shugaban na farar hula.
Masu aiko da rahotanni sun ce, ɗaukar matakin soji kan lamarin zai iya zama mai wahala sosai, saboda kayan aiki, da kuma hadari, domin zai iya kara dagula al’amura a yankin, wanda masu ikirarin jihadi ke yi wa ta’annati.