Gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokin ta da na Nijar

0
149
Iyakar Najeriya da Nijar
Iyakar Najeriya da Nijar

Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar cikin gaggawa saboda tabarbarewar siyasar da ake fama da ita a kasar.

Manufar umarnin a cewar Mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adeniyi Adewale, za ta amfanar kasashen biyu.

Adewale, wanda ya kasance a kan iyakar Jibia a jihar Katsina, domin sanya ido kan matakin da ake bi, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta umarci masu ruwa da tsaki a harkokin kan iyakokin da su tabbatar da bin ka’idar umarnin.

“Kamar yadda muka sani, shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu dan gwagwarmaya ne na hadakar tattalin arziki a yammacin Afirka. Ya yi imanin cewa kasuwanci da makwabciyarmu zai iya kawo ci gaba ga ‘yan Nijeriya da sauran jama’ar yankin,” in ji shi.

“Watakila wannan mataki ya taimaka masa wajen samun nasararsa a matsayin shugaban ECOWAS cikin wata guda da hawansa shugabancin Nijeriya.

“Yanzu, muna da wani yanayi a hannunmu inda ake fama da rashin zaman lafiya da rashin tsaro. Wannan yanayin ba zai ba da damar bunkasar ciniki ba. Ba za mu iya samun kasuwanci mai ma’ana ba a cikin yanayi na rashin tsaro da rashin zaman lafiya da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.

“Don haka ne kungiyar ECOWAS, ta hannun ikon shugabanta, ta dauki matakin rufe dukkan iyakokin kasa da Jamhuriyar Nijar.”

A cewarsa, hukumar ta tura jami’ai kan iyakokin Nijeriya da Nijar don tabbatar da tsaro.

“Hakki ne da ya rataya a wuyan hukumar Kwastam ta Nijeriya, tare da yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati, don aiwatar da abin da ya dace.

“Hukumar kwastam ta Nijeriya ta yi hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro a kan iyaka domin aiwatar da dokar rufe iyakokin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here