HOTUNA: Dubban ‘yan Nijar sunyi dandazon nuna goyon bayan mulkin sojoji a kasar

0
209

Dubban ‘yan Nijar ne suka taru a filin wasa na Général Seyni Kountche da ke birnin Yamai don nuna goyon bayansu ga sojojin da suka yi juyin mulki a ranar Lahadi

Tun washegarin da sojoji suka yi juyin mulkin wasu suka fara zanga-zangar goyon baya da kuma ta adawa da su. 

Lamarin na zuwa ne yayin da wa’adin da ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ta bai wa sojojin ya cika – kan ko dai su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki ko kuma su fuskanci ƙarfin soja. 

Tuni mambobin ƙungiyar suka rufe iyakokinsu tare da yanke duk wata hulɗa da Nijar ɗin, yayin da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea suka ayyana goyon bayansu ga sojojin na Nijar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani. 

Najeriya, babbar ƙawar Nijar, ita ce ke jagaorantar yunƙurin tilasta wa sojojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here