Kasurgumin mai laifi da rundunar yan sandan Kano ke nema ya mika wuya

0
183

Wani kasurgumin mai laifi da ake nema ruwa a jallo, Nasiru Abdullahi wanda aka fi sani da Chile Maidoki, ya mika wa hukuma kansa a Jihar Kano.

Maidoki na daya daga cikin fitattun masu laifi da Rundunar ’Yan sanda Jihar Kano ke nema ruwa a jallo kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Mutumin da ake zargi dai mazaunin Layin Falwaya ne a Unguwar Kurna, wanda Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Mohammed Usaini Gumel ya sanya tukwicin N100,000 ga duk wanda ya taimaka wajen kama shi.

Sai dai kwatsam Maidoki ya saduda, inda ya mika kansa a Babbar Shelkwatar ’Yan sanda da ke Bompai a wannan Asabar din.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Kano SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ya ce a yanzu adadin tubabbun masu laifi da suka mika wuya a jihar ya kai 100.

A cewar Kiyawa, Chile Maidoki ya shaida musu cewa yana kwana a makabartu da ke cikin Birnin Dabo domin kaucewa fadawa hannun jami’an tsaro.

SP Kiyawa ya ce Maidoki yana neman ’yan sanda da kuma jama’ar Kano da su yi masa afuwa, la’akari da cewa ya tuba kuma a shirye yake wajen taimaka wa ’yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.

SP Kiyawa ya ce Maidoki yana neman ’yan sanda da kuma jama’ar Kano da su yi masa afuwa, la’akari da cewa ya tuba kuma a shirye yake wajen taimaka wa ’yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.

A kan haka ne SP Kiyawa yake jan hankalin al’umma da su kiyaye wajen tsangwamarsa.

Ya kara da cewa, “har yanzu tukwicin N100,000 da aka yi alkawari na nan ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaki wajen cafke sauran mutanen biyu da ake nema ruwa a jallo —Abba Burakita na Unguwar Dorayi da Hantar Daba na Kwanar Disu.

“Duk wani mai bayani a kan wadannan ababen zargi ya gaggayta garzayawa ofishin yan sanda mafi kusa,” a cewar Kiyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here