‘Labarin tura ‘yan NYSC zuwa Nijar ba gaskiya ba ne’

0
166

Hukumar yi wa ƙasa hidima, National Youth Service Corps (NYSC), ta ce babu wani shiri da take yi na tura matasan masu hidimar ƙasa zuwa Jamhuriyar Nijar don yaƙar sojojin da suka yi juyin mulki. 

Kakakin NYSC, Mista Eddy Megwa, ya ce sun musanta batun ne sakamakon wani bidiyo da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, kamar yadda kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito. 

“Babu ƙanshin gaskiya a labarin da wani mai shirya barkwanci ya ƙirƙira,” in ji shi. “Ya kamata masu yi wa ƙasa hidima da iyaye su yi watsi da batun, wanda aka shirya shi da zimmar tayar da zaune tsaye.” 

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro za su kama wanda ya ƙirƙiri bidiyon. 

A ranar Juma’a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi goyon bayan majalisar ƙasar don tura sojoji ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas zuwa Nijar don su tilasta wa sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum komawa kan tsarin mulki. 

Sai dai majalisar ba ta goyi bayan ƙudirin ba, tana mai ba da shawarar a ci gaba da yunƙurin tattaunawa ta hanyar difilomasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here