Dije Aboki: Mace ta farko da ta zama alkaliyar alkalan Kano

0
204

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mai Shari’a Dije Abbu Aboki a matsayin alƙaliyar alƙalai ta Kano a yau Litinin. 

Ita ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin, kuma an yi bikin ne a fadar gwamnatin Kano bayan majalisar dokoki ta amince da naɗin ta a farkon watan Yuli. 

Da yake jawabi bayan rantsuwar, Gwamna Kabir ya ce an naɗa ta ne “saboda kyawawan ayyukanta wajen tabbatar da adalci a harkokin shari’a”. 

“Kin nuna ƙwarewarki a tsawon shekarun aikinki a matsayin babbar mai shari’a da ta himmatu wajen yin adalci,” a cewarsa. 

Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne bisa rakiyar mijinta Abdu Aboki, wanda shi ma tsohon alƙali ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here