Juyin mulki: Tsamin dangantaka na kunno kai tsakanin Najeriya da Nijar

0
211
Iyakar Najeriya da Nijar
Iyakar Najeriya da Nijar

‘Yan Najeriya mazauna Nijar sun yi taro da nufin gamsar da ‘yan kasar ta Nijar tasirin kasar, da ma  karfin huldar da ke tsakanin kasashen, su na masu bayyana cewa ba da sunansu kungiyar CEDEAO ta bai wa sojojin Nijar wa’adi ba. 

AGADEZ, NIGER – Yanzu haka ‘yan Najeriya da ke gudanar da kasuwancinsu a sun bayyana damuwa kan halin da Nijar ta shiga bayan juyin mulki tare da yin kira ga bangarorin da su bi hanyoyin tattaunawa domin samun mafita.

Tun bayan kifar da Gwamnatin dai dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar ke ci gaba da tsami, musamman bayan da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, wacce Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ke jagoranta ta kakaba wa Nijar takunkumin karya tattalin arziki, da ma bayyana daukar matakin anfani da karfin soja akan sojojin da su ka yi juyin mulki a Nijar, mafari kenan da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Nijar ta gudanar da taro da nufin bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

To saidai ‘yan Najeriya da ke gudanar da harkokin kasuwanci a Nijar sun bayyana damuwa kan halin da Nijar ke ciki wanda zai iya kawo musu cikas ta bangaren kasuwancin da suke gudanarwa.

Ibrahim Mohamed shugaban matasan kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Nijar ya yi kira ga ‘yan uwansa matasa da su kauce wa duk wasu kalamai da za su tada fitina a tsakanin al’umma sakamakon irin yanayin da kasar ta Nijar ke ciki halin yanzu.

‘Yan Najeriya da dama a nasu bangare suna kiraye-kiraye ga hukumomi da kuma Kungiyar ta ECOWAS akan su kauce wa daukar matakin da zai tsunduma yankin Afurka ta yamma cikin wani yaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here