DA DUMI-DUMI: Majalisa ba ta tabbatar da El-Rufai, wasu mutum 2 a matsayin ministoci ba

0
187

Majalisar dattawa ta kammala tantance mutane 45 daga cikin 48 da shugaba Bola Tinubu ya nada a matsayin ministoci, inda ta tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar ministoci bayan mako daya na tantancewa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanya sunayen nadin zuwa jerin kuri’u, inda aka amince da su .


Sauran wadan suke jiran tantancewa sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Stella Okotete (jihar Delta), da Abubakar Danladi (jihar Taraba), inda har yanzu ana ci gaba da binciken tsaro akansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here