Zulum ya raba kayan abinci don rage matsin rayuwa

0
216

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanya ido kan shirin rage raɗaɗi da ya ƙunshi tallafin abinci ga iyalai 2,000 a mazaɓar Mafoni da ke birnin Maiduguri.

Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau mai magana da yawun gwamnan ya fitar ta ce manufar rabon abincin ita ce rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, kuma yayin rabon an bai wa kowanne gida buhun shinkafa da wake biyu.

Zulum ya bayyana cewa an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar shirin ne daga mazaɓa 27 daga faɗin Maiduguri da kuma mazaɓa 12 daga ƙaramar hukumar Jere.

Sanarwar ta ce rabon abinci wanda ya ƙunshi buhun shinkafa 54,000 da buhunnan wake 54,000, an bayar ne ga magidantan da suka fi buƙata a cikin ƙananan hukumomin jihar biyu, a cewar gwamnatin. 

Ta ƙara da cewa gwamnatin Zulum ta tashi haiƙan wajen neman dabarun da za su rage illar da hauhawar farashin man fetur ta haifar a kan talakawa, ta hanyar tabbatar da ganin abinci da sauran muhimman ayyuka ga masu tsananin buƙata.

Da yake jawabi a wurin raba abincin, Gwamna Zulum ya ce buhunnan shinkafar wani ɓangare ne na shinkafa buhu 3,000 da gwamnatin Borno ta karɓa daga Shugaba Bola Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here