Manchester United da West Ham United sun cimma yarjejeniyar cinikin dan wasa Harry Maguire.Â
A satin da ya gabata ne, West Ham ta taya dan wasan mai shekara 30 a duniya a kan kudi fam miliyan 20 sai dai nan take Manchester United ta yi fatali da tayin, inda ta ke neman a bata fam miliyan 40.
Sai dai daga baya West Ham ta sake sabon tayi na fam miliyan 30 shi ma United ta ce ba za ta siyar a haka ba.
Da safiyar yau ne kuma, kungiyoyin biyu suka cimma matsaya a kan fam miliyan 30 din kuma yanzu dan wasan zai tattauna batun albashi da kungiyar da ke birnin Landan.
A 2019 ne Manchester United ta kashe fam miliyan 80 wajen sayen dan wasan daga Leceister City.