Takunkuman da aka lafta wa Nijar sun gurgunta ayyukan jin kai a sassan kasar

0
164

Majalisar Dinkin Duniya ta ce juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, da kuma matakan takunkuman ECOWAS da suka biyo baya na yanke hulda da rufe iyaka, sai kuma rufe filayen jiragen sama da sojoji suka yi, sun gurgunta ayyukanta na jin kai a sassan kasar.

Shugabar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijar Louise Aubin, ta ce yanzu haka matakin rufe iyakokin na Nijar na barazana ga isar da tallafin abinci da magunguna ga mabukata a yankunan Nijar.

Jami’ar ta yi gargadin cewa yanzu haka hukumomin da suka hada da UNICEF, da UNFPA da kuma WFP, na ta fafutukar cike gibin kayayyakin tallafin da suke ka iwa jama’a agaji da su, wadanda ke gaf da yin karanci.

Kididdiga ta nuna cewar gabanin juyin mulkin da sojoji  suka yi a Nijar, mutane miliyan 4 da dubu 300 Majalisar Dinkin Duniya ke shirin rabawa tallafin abinci da magunguna, amma a halin yanzu akwai yiwuwar adadin ya karu matuka cikin lokaci kadan.

Tuni dai sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka gargadi ‘yan kasar da su kasance cikin shirin fuskantar yanayi mai tsauri cikin makwanni ko kuma watannin da ke tafe, bayan da suka sha alwashin jurewa duk wani irin matsin diflomasiya daga kasashen ketare, tare da zama cikin shirin ko ta kwana na kare kansu daga yiwuwar kaddamar da karfin soja akansu.

A ranar Lahadin da ta gabata, wa’adin kwanaki  bakwai ya kare, wanda kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin na Nijar kan su mayar da Bazoum Mohammed da suka hambarar kan kujerar jagorancin kasar.

Biris din da sojojin na Nijar suka yi  da wa’adin ne ya sanya ECOWAS din ko CEDEAO kakaba wa kasar karin takunkumai a ranar Talata, baya ga rufe iyakokin kasa da na sama da kasashen kungiyar ta yammacin Afirka suka yi da Jamhuriyar ta Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here