Tun kafin isowar damunar, hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi da dama na kasar a ciki har da na jihohin Nejan.
Daruruwan gonaki ne hade da amfani gona mai dumbin yawa suka salwanta a jihar Nejar Najeriya sanadiyyar ambaliyar da ta aukawa wasu kananan hukumomi.
Wannan al’amari dai ya jefa dubban manoma cikin yanayi na tashin hankali tare da fargabar kara samun karancin abinci a wannan shekara.
Tun kafin isowar damunar, hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi da dama na kasar ciki har da Jihar Nejan.
Alh. Shehu Yusuf Galadima Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta jihar Neja ya ce sun tabka asara ta miliyoyin Naira a sakamakon yadda ambaliyar ta yi awon gaba da gonakin masara da na shinkafa.
Ita ma dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja ta ce ba ta gama tantance yawan gonakin da ambaliyar ta mamaye ba a cewar mukaddashin Darakta na hukumar a jihar Neja Malam Garba Salihu.
Har ila yau dai Hukumar Bada Agajin ta ce akwai yiwuwar kara samun ambaliyar a nan gaba saboda haka jama’a su kula inji Malam Garba Salihu.
Yayin da aka tabka asara gonaki a sakamakon ambaliyar a jihar Nejan, a gefe guda kuma ‘yan bindiga ne suka hana manoma zuwa gonakin al’amarin da masu sharhi ke ganin matsalar babbace saboda haka akwai bukatar daukar kwakkwarar mataki.