An hallaka mutane da dama a wani sabon hari da aka kai Filato

0
192
Map-of-Plateau-State

Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Filato ta ce a ƙalla mutum 21 ne a kashe a wani sabon hari da aka kai a ƙauyuka biyu a jihar.

Ƴan bindiga sun mamaye ƙauyen Barkin Ladi da sanyin safiyar Alhamis, inda suka harbe mutum 17.

Bayan wani ɗan lokaci an sake harbe mutum huɗu a wani harin da ƴan bindigar suka kai wani ƙauye da ke kusa da Barkin Ladin.

Kashe-kashen na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke luguden wuta cikin dazukan da ke zargin maɓoya ce ta ƴan ta’adda a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawo ƙarshen hare-haren da yayi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane tun daga watan Mayu.

Ƙungiyoyin fararen hula sun ɗora alhakin kashe-kashe kan makiyaya, inda suka ce suna yin hakan ne domin tarwatsa manoman yankin don samun damar mamaye filayensu.

Sai dai babu tabbaci ko ƙungiyoyin makiyayan sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan zargi.

Jihar Filato daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci da addini, da kuma na manoma da makiyaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here