Hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC ta bayyana cewa, ta bankado haramtattun matatun man fetur sama da 100 a shekaru biyu da suka wuce.
Kwamandan Janar na hukumar, Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa hakan a yayin da ya kai ziyarar aiki a hukumar NMDPRA da ke Abuja a jiya Laraba.
A cewarsa, tun lokacin da ya kama aiki a matsayin Kwamandan NSCDC sun kuma kama nutane da ake zargi sama da 200 bisa aikata lafin satar mai, inda 100 daga cikinsu, an hukunta su.
Kazalaika ya ce, NSCDC babu wata tantama ta samu nasara wajen yakar masu fasa bututun mai a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Audi, ya kuma bai wa hukumar ta NMDPRA tabbacin cewa, hukumar sa za ta ci gaba da ba ta hadin kai domin ta samun nasara a kan ayyukanta da ta sa a gaba.
A nasa jawabin Darakta Janar na NMDPRA, Mallam Bashir Sadiq, ya yaba wa NSCDC bisa kokarin da ta ke yi na bai wa manyan kadarorin kayan gwamnatin tarayya.
Ya kuma yi kira ga hukumar kar ta gajiya wajen sauke nauyin da aka dora mata kamar yadda dokar kasar nan ta tanadar.