Ko ganawar da malamai da sarakuna suka yi da Tinubu zai yi tasiri kan fasa auka wa Nijar?

0
235

Duk da nanata matakin ci gaba da barin duk ƙofofi a buɗe, don magance rikicin juyin mulkin Nijar, umarnin Ecowas na ɗaura ɗamarar dakarunta na ko-ta-kwana don auka wa ƙasar, sanyaya gwiwar masu fatan ganin dambarwar ba ta kai ga fito-na-fito ba ne.

Haka zalika, umarni guda biyu da ta bayar ga sojojinta a cikin sanarwar bayan taron Abuja ranar Alhamis, suna da tayar da hankali da kuma raba hankalin.

Ecowas dai ta umarci kwamitin manyan hafsoshin tsaro ta shirya dakarun ko-ta-kwana na Ecowas cikin ɗamara da duk al’amuransu nan take.

Ta kuma umarci tura dakarun ko-ta-kwana, su dawo da aiki da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.

A jajiberen taron gaggawar wanda ƙasashen Ecowas 12 suka halarta, kai-kawon wasu malamai da wasu masu sarauta daga Nijar da Najeriya, ya ƙarfafa gwiwar cewa mai yiwuwa shugabannin al’ummar suna iya buɗe ƙofar da ta gagari jami’an diflomasiyya.

Khalifa Muhammadu Sanusi na II da Sarkin Damagaram Sultan Abubakar Sanda Umarou sun samu shimfiɗar fuska a birnin Niamey har ma sun gana da jagoran juyin mulkin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, kafin da yamma Khalifa ya sauka a Abuja, fadar Shugaba Tinubu.

Yana ɗaya daga cikin mutanen ƙasashen waje ƙalilan da suka gana da sabon shugaban mulkin sojin na Nijar.

A ɓangare guda kuma, Majalisar malaman addinin Musulunci a Najeriya ta gana da shugaban Najeriya, har ma sun shaida masa cewa ba sa goyon bayan amfani da ƙarfin soja a rikicin siyasar Nijar.

Malaman ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, babban jagoran ɗarikar Tijjaniya da sakataren Jamaatu Nasrul Islam (JNI), Farfesa Khalid Abubakar, sun nusar da Tinubu game da buƙatar ci gaba da ƙoƙarin sasanta lamarin ta hanyar difilomasiyya, maimakon ƙarfin soja.

“Najeriya da Nijar kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai, in ji Farfesa Khalid Abubakar. “Yan’uwa muke, addininmu ɗaya, al’adunmu ɗaya. Dole a bi a hankali don a samu zaman lafiya.”

Khalifa Muhammad Sanusi dai ya bayyana ƙarara cewa ziyarar da ya kai Nijar, wani yunƙuri ne na ƙashin kansa, kuma yana ganin kowanne ɗan Najeriya ma yana da gudunmawar da zai iya bayarwa don shiga tsakanin da zai hana Ecowas da Nijar kai ruwa rana.

Khalifa Sanusi
Bayanan hoto,Khalifan Tijjaniya Muhammadu Sanusi ya gana da shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani.

Zuwa yanzu dai ba za a iya ce taƙamaimai ga nasarar da irin waɗannan ziyarce-ziyarce da sarakuna da malamai suka gudanar a yunƙurin hana gwabza yaƙi, musamman bisa la’akari da sanarwar bayan taron Ecowas na Abuja.

Duk da haka, ison da Khalifa Sanusi na II ya samu a fadar shugaban ƙasa ta Niamey kawai ya isa cusa kyakkawan fata a zukata na cewa, idan irin wannan ƙoƙari ya ci gaba, mai yiwuwa ɓangarorin biyu na iya tanƙwarowa har su yarda su sake buɗe ƙofa ga tattaunawa da masalahar diflomasiyya.

Ya dai ba da tabbacin cewa: “Za mu ci gaba da ƙoƙari wajen ganin ɓangarorin biyu sun fahimci juna. Yanzu ba lokaci ba ne, na bar wa gwamnati tattaunawar diflomasiyya. Ya kamata dukkan ƴan Najeriya su shiga a dama da su”.

Ziyarar tasa ta zo ne kwanaki ƙalilan bayan wata makamanciyarta da ayarin Ecowas ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), tsohon shugaban Najeriya ya kai Nijar, ya kai ba tare da ya samu ganawa da Janar Tchiani ba.

Haka zalika, sojojin masu juyin mulki sun kuma hana wasu jami’an Ecowas da na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma na Tarayyar Afirka damar sauka a Niamey.

Sanarwar da Ecowas ta wallafa a shafinta na sada zumunta, na cewa jami’an ɓangarorin uku sun soke tafiyar da shirya bayan sun samu bayani da tsakar dare cewa sojojin Nijar ba sa maraba da ziyararsu.

Wasu msharhanta kamar Ambasada Suleiman Ɗahiru na ganin cewa matakan da Ecowas ta ɗauka cikin gaggawa, na ƙaƙaba wa Nijar takunkumai da yi mata barazana da yaƙi, jim kaɗan bayan hamɓarar da gwamnatin Bazoum a watan Yuli, mai yiwuwa sun harzuƙa shugabannin juyin mulkin.

Yana cewa kamata ya yi ƙungiyar ƙasashen ta bi komai daki-daki. A ƙure bin hanyoyin diflomasiyya, kafin a fara zance sanya takunkumai har ma a je ga batun amfani da ƙarfin soja.

Sai dai ga dukkan alamu, shugabannin Ecowas ba su da wannan lokacin, ƙungiyar na fuskantar matsin lamba bayan jerin ƙwatar mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea a cikin ‘yan shekaru.

A yanzu tana so ta nuna ƙarara cewa, ba za a sake lamuntar karɓar mulki da ƙarfin bindiga ba, a Afirka ta Yamma.

Sai dai, wasu manyan ‘yan boko ƙwararru a Najeriya sun rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Shugaba Tinubu, suna jan hankalinsa a kan ya yi taka-tsantsan wajen ɗaukar matakan mayar da Nijar kan turbar dimokraɗiyya.

Wasiƙar daga mutanen da suka kira kansu ‘yan ƙasan da suka damu ta ce akwai buƙatar Najeriya ta riƙa sara tana duban bakin gatari game da abin da ke faruwa a Nijar.

Ƙwararrun dai sun jaddada goyon bayansu ga yin amfani da sarakuna da malaman addini da kuma ƙungiyoyi, wajen shiga tsakani da neman masalaha a ƙoƙarin kaucewa duk wani abu da zai ta’azzara rikici.

Sarakuna da malamai a Najeriya sun sha ba da irin wannan gudunmawa ta shiga tsakani a duk lokacin da ƙasar ta tsinci kanta cikin wata turka-turka ko wani rikicin diflomasiyya musamman da ƙasashen Larabawa.

Tasirin sarakuna da malamai wajen shiga tsakani

Masana irinsu Dakta Kole Shettima na ganin wannan yunƙuri da Malamai da Sarakuna da kuma shugabannin addinin Kirista ke yi, na da matuƙar muhimmanci saboda su ne jagororin al’umma, kuma ƙaunar ganin jama’arsu sun shiga wahala.

Dakta Kole ya ce malaman sun ga cewa matakin da za a ɗauka zai iya cutar da al’ummominsu wanda shi ne ya sa suka tashi haikan don shiga tsakani.

“Yanzu da aka katse wutar lantari da ake bai wa Nijar ai ba gwamntin Najeriya ce ke asara ba, kamfanin da take ɗaukar wutar daga Najeriya ita ke asara,” in ji Dakta Kole.

Ya ce tasirin da ƙoƙarin shiga tsakani da malamai da kuma sarakuna ke yi ba zai misaltu ba.

“Irin martaba da sarakuna ke da shi ne ya sa ka ga sojojin sun gana da Khalifan Tijjani na Afrika Muhammad Sanusi”.

Masanin ya ce shugabannin addinin na da rawar da za su taka waje tabbatar da ba a bar ba wa shugabanni kaɗai su ja ragama ba.

“Ya kamata al’ummomin ƙasashen duka su tashi wajen ganin ba a bar rikici ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu ba saboda daɗaɗɗiyar alaƙa da take tsakaninsu,” in ji Dakta Shettima.

Ya ce ko da ba a samu abin da ake so a shiga tsakanin ba, to fa ba bu wanda zai fito ya zargi malaman da kuma sarakuna cewa ba su bayar da gudummawa ba a ƙoƙarin shawo kan matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here