Gwamnatin Kano ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar baki daya

0
186
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin duk wasu makarantu masu zaman kansu da ke aiki a jihar.

An yanke hukuncin ne a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu makarantu masu zaman kansu.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu, Alhaji Baba Abubakar Umar ne, ya bayyana cewa ana bukatar dukkan makarantu masu zaman kansu da su yi sabuwar rajista cikin gaggawa.

Umar ya bayyana cewa matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya na gudanar da ayyukansu.

“An tunatar da masu makarantu masu zaman kansu alhakin da ya rataya a wuyansu na biyan harajin kashi 10 ga gwamnati. Wannan kudi ko yaushe yana habaka ci gaba a fannin,” in ji shi.

Mashawarcin na musamman ya tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa zai tabbatar da adalci wajen kula da ayyukan makarantu masu zaman kansu.

Ya jaddada bukatar aiwatar da ka’idojin aiki ga masu mallakar makarantu masu zaman kansu wadanda suka hada da kayan aiki, yanayin koyo, manhaja da jadawalin koyarwa.

Ya kuma tabbatar wa iyaye fifikon da aka ba su wajen kiyaye muradunsu da na ‘ya’yansu.

Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu a jihar, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka, yana mai kallon matakin a matsayin abin yabawa a fannin ilimi a jihar.

Adamu ya bayyana muhimmancin yanayin tsarin aiki, yana mai tabbatar da cewa duk wani aiki da ba a bin ka’ida yana samun koma baya.

Ya yi kira ga masu makarantu masu zaman kansu da su hada kai da gwamnati wajen gudanar da sauye-sauyen.

A yayin taron an fitar da wata sabuwar manhaja domin tattara bayanan masu makarantu masu zaman kansu a fadin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here