An gudanar da zanga-zangar goyon bayan ECOWAS  a Katsina

0
154

Wata kungiyar matasa ta gudanar da zanga-zangar goyon bayan ECOWAS a Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya ranar Asabar.

Kungiyar Coalition of Pro-Democracy Activists ta ce mambobinta sun nuna goyon bayan su dari bisa dari ga ECOWAS da gwamnatin Nijeriya kan matakan da suka dauka na saka wa sojojin Nijar takunkumai saboda juyin mulkin da suka yi.

Sannan kuma sun yi Allah wadai da wadanda suka yi juyin mulkin.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga sojojin su gaggauta mika mulki ga farar-hula, haka kuma sun yi kira a saki Mohamed Bazoum da ke tsare.

Har yanzu dai ba a zauna kan teburin sulhu na tsakanin ECOWAS da sojojin Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar wanda takunkumi ya biyo baya.

Sai dai kungiyar ECOWAS ta yi ta tura wakilai domin shawo kan sojojin Nijar din kan hawa teburin sulhu.

Ko a makon da ya gabata sai da Sarki Muhammad Sanusi II ya je Nijar din inda ya tattauna da shugaban mulkin soji na kasar.

Haka kuma tawaga ta musamman ta malamai daga Nijeriya ta je Nijar din a ranar Asabar, inda shugaban sojojin ya ce ya yarda za su yi sulhu da ECOWAS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here