Dalilin da ya sa muka fara kama masu tallar maganin gargajiya a Kano – El-Mustapha

2
240

Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha ya ce hukumarsu ta fara kamen masu sayar da maganin gargajiyar da ke amfani da batsa wajen tallansu.

Ya kuma ce kamen ya hada har da masu tallan da ke amfani da hotunan da ba su dace ba da nufin tallata magungunansu don su ja hankalin masu siya.

Abba, a cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Asabar ya ce shugabancin sa ba zai zuba wa wannan halayya ido ta cigaba da faruwa a Jihar ba.

Ya ce amfani da kalaman batsa ya saba wa tarbiyar Jihar tare da koyarwar addinin addinin Musulunci.

Abba na yin wannan jawabi ne a gaban harabar hukumar, jim kadan bayan kammala aikin kaman masu maganin gargajiyar da aka samu da laifin saba dokar hukumar.

An gudanar da kamen ne a wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami’an ’yan sanda da ma’aikatan hukumar a Kano.

Abba ya ce doka ce taba wa hukumar damar gudanar da wannan aiki don haka za ta yi wa dokar biyayya sau da kafa domin cim ma nasara.

2 COMMENTS

  1. Wannan Al’amarin yayi Dai-Dai, saboda haka suke shigowar cikin Unguwa inda Kananun Yara suke da irin wannan Tallan

  2. Gaskiyane wanan allah ya taimakeku yabada sa a kuma muna goyan bayan a dakar da duk wanda zai bata tarbiyar yan jahar kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here