Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yarda su yi sulhu da ECOWAS

1
483

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce a shirye suke su tattauna da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Sabon Firaiministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan tawagar Malaman Nijeriya ta ziyarci jagoran masu juyin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani ranar Asabar a Yamai.

Wannan ne karon farko da sojojin suka nuna alamar yin sulhu tun bayan da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Tattaunawa nan da kwanaki masu zuwa

A lokacin da ‘yan jarida suka tambayi Firaiministan kasar kan ko sojojin sun shirya yin sulhu, ya ce: “Eh, tabbas. Wannan shi ne abin da jagoranmu ya gaya wa (Malaman), bai ce ba zai yi sulhu ba.”

Firaiministan ya ce yana fata nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa za su soma tattaunawa da ECOWAS.

“Mun amince (mu tattauna) kuma shugaban kasarmu ya yarda a yi sulhu. Yanzu za su koma gida su shaida wa shugaban Nijeriya abin da muka gaya musu…muna fata nan da kwanaki masu zuwa, su (ECOWAS) za su zo nan su gana da mu kan yadda za a cire mana takunkumai,” in ji shi.

Tawagar Malaman ta ce ta ‘samu nasara’ a ziyarar da ta kai Yamai./Hoto: OTHER

Firaiminista Lamine ya bayyana takunkuman da ECOWAS ta sanya wa kasar, wadanda ya ce sun jefa su cikin mawuyacin hali, a matsayin “rashin adalci”.

Ya kara da cewa takunkuman sun saba dokokin kungiyar ta ECOWAS. Sai dai ya ce ba za su amince a gindaya musu wani sharadi kafin a cire takunkuman ba.

Sojojin sun nemi afuwa kan kin sauraren tawagar tsohon shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar wadda ta soma zuwa Yamai don yin sulhu da su.

‘Ziyararmu ta yi nasara’

Shugaban tawagar Malaman, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa manema labarai cewa sun je Nijar ne “domin yin sulhu”. Ya ce sun gaya wa jagoran masu juyin mulkin muhimmancin tattaunawa game da wannan rikici na siyasa.

Sheikh Bala Lau ya ce kafin su tafi Nijar sun je wurin shugaban Nijeriya wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS Bola Tinubu inda suka gaya masa cewa bai dace a yi amfani da karfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar ba.

Ya ce sun samu “nasara” a ziyarar da suka kai wa sojojin.

Amma ya ce ba su gana da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba domin hakan ba ya cikin abubuwan da ziyarar tasu ta kunsa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here