Rufe iyakar Nijar: ‘Yan kasuwar Najeriya na asarar biliyan 13 a duk mako

0
204
Iyakar Najeriya da Nijar
Iyakar Najeriya da Nijar

‘Yan kasuwa daga arewacin Najeriya sun koka kan yadda suke tafka asarar kimanin Naira biliyan 13 a duk mako sakamakon rufe kan iyakar Jamhuriyar Nijar.


Tun a ranar 4 ga watan Agusta ne, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin rufe kan iyakokin Nijar da suka hada da na Jibiya da ke Katsina da Illelah da ke jihar Sokoto da kuma Maigatari da ke jihar Jigawa.

A yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, shugaban Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Arewa ta Arewa Economin Forum, Ibrahim Yahaya Dandakata ya bayyana cewa, ‘yan kasuwar sun gaza jure wa radadin rufe kan iyakokin, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta bude kan iyakar Maje-Illo da ke jihar Kebbi domin bai wa ‘yan kasuwar damar shigo da hajojinsu cikin Najeriya.

Tun lokacin da shugaban kasa ya bada umarnin rufe kan iyakokin Janhuriyar Nijar bayan sanar da juyin mulki, tasirin matakin ke tsananta. ‘Yan kasuwar Arewa na tafka asarar naira biliyan 13 a duk mako. Inji Dandakata.

Kungiyar ta Arewa Economic Forum ta kiyasta cewa, ana kulla cinikayyar dabbobi da kayan abinci da ta kai ta naira biliyan 177 a duk shekara tsakanin ‘yan kasuwar Najeriya da Nijar.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da ya bayyana sunansa a matsayin Hamza Saleh Jibiya ya bayyana cewa, akwai akalla motocin kwantena dubu 2 makare da kayan gwari da sauran kayan abinci da suka makale a kan iyakokin.


Ya ce, akalla darajar kudin kowacce kwantena ta fara ne daga dala dubu 20 zuwa dala dubu 70, abin da ya ce a lissafinsu ya kai naira biliyan 140.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here