Jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a Najeriya

0
176

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta yi gargadi, cewa jihohi 19 da garuruwa 56 a sassa daban-daban na kasar, za su yi fama da mamakon ruwan sama, wanda zai iya haddasa ambaliya a cikin wannan wata na Agusta da ake ciki.


Don haka an bukaci jama’a, musamman ma wadanda ke zaune a wuraren da abin zai shafa da su zauna cikin shiri.


Bashir Idris Garga, wanda shi ne babban jami’in kai dauki na hukumar NEMA, ya shaidawa BBC cewa gardagin ya biyo bayan kididdigar da hukumar yanayi ta kasar ta fitar.

“Tun daga 14 zuwa 18 kamar yada hasashen yanayin na watan Agusta na wannan shekarar ya nuna, za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya,” in ji shi.

Hukumar ta NEMA ta ce jihohin da alamarin zai shafa sun hada da Delta da Ekiti da Ondo da Lagos da Anambra da kuma Ogun.


Sauran su ne Nasarawaa, kuros Ribas da Bauchi da Jigawa da Osun da Zamfara da Sokoto da Adamawa da Taraba da Binuwai da Imo da kuma Abia.


Ta ce ruwan sama da za a tafka zai shafi garuruwa 56 dake cikin wadannan jihohi kuma tuni ta nemi gwamnattocin wadannan jihohin da su dauki matakai na musaman.


Alhaji Garga ya kuma bayyana cewa tuni aka fara samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wadannan wurare:


“ A cikin kwanaki uku da suka wuce ana ta ruwa ba bu kakkautawa, kuma a duk lokacin da aka ci gaba ruwa irin wannan, yawancin matattarar ruwan da kuma dam-dam suna cika, sai su tumbatsa inda za su amayar da wannan ruwan, daga bisa ni kuma ya je ya yi barna,” in ji shi.


Hukumar ta NEMA ta yi gargadin cewa gonakai da gidaje da wasu ma’aikatu za su fada cikin wannan iftilai.


Ta kuma yi kira ga mutane da su zauna cikin shiri, kuma a dauki matakan yashe magudanan ruwa, tare da inganta yanayin wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here