Sabbin tuhume-tuhume da gwamnatin tarayya zata yiwa Emefiele

0
176

Gwamnatin tarayya ta ce za ta janye tuhumar mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da ta shigar kan dakataccen gwamnan babban bankin Æ™asar Gowdin Emefiele, da kuma shigar wasu sabbin tuhume-tuhume akansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

A ranar 25 ga watan Yuli ne, wani alkali ya bayar da belin Emefiele kan naira miliyan ashirin kan wasu zarge-zarge guda biyu da ake yi masa, da ya haÉ—a da zargin mallakar makamai, inda ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali a Ikoyi, har sai ya cika sharuÉ—an belin.

Sai dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake kama shi bayan wani artabu da jami’an gidan yari.

A ranar Talata, darektan shigar da Æ™ara na ma’aikatar shari’a, Mohammed Bakodo, ya faÉ—a wa mai shari’a Nicholas Oweibo cewa ya ce za a yi wa Emefiele sabbin tuhume-tuhume ne bayan Æ™arin bincike da aka gudanar.

Sai dai lauyan da ke kare wanda ake kara, Joseph Dauda, ya nuna adawa da hakan, inda ya kalubanci cewa gwamnati ta ki bin umarnin kotuna na buƙatar sakin Emefiele.

Da yake magana da manema labarai, Abubakar ya ce an shigar da sabbin tuhume-tuhumen ne a wata Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

ÆŠaya daga cikin sabbin tuhume-tuhumen na zargin Emefiele da bai wa kansa haramtattun damarmaki ta haramtacciyar hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here