Tinubu na duba yiwuwar dawo da tallafin mai na wucin gadi

0
189

Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar dawo da bayar da tallafin man fetur na dan wucin gadi biyo bayan matsin rayuwa da aka shiga da kuma yadda farashin Dalar Amurka ke ta hauhawa tun bayan cire tallafin a watan Mayu, Inji jaridar TheCable

Har yanzu dai shugaban bai tabbatar da wannan kuduri ba amma takardar shawarar tana kan teburinsa, kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa TheCable.

Tuni dai kungiyoyin kwadago suka yi barazanar shiga yajin aiki na sai Baba-ta-gani idan farashin man fetur ya kara hauhawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here