Wike ya ziyarci Ganduje a hedikwatar APC

0
190

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, wanda aka tantance domin zama minista, Nyesom Wike, ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Umar Ganduje a ofishin jam’iyyar.

Ganduja ya karbi bakuncin Wike a ofishinsa ne yayin da ake rade-radin yana shirin sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC. Sai dai ya sha musanta shirin komawa jam’iyyar mai mulki.
Wike wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC ya mika sunansa a cikin jerin ministocin da zai nada ya fito karara ya yaki dan takarar shugaban kasan PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar.

A yayin wani bikin da aka shirya masa bayan ya mika mulki ga zababben gwaman jiharsa, Simi Fubara, an ji gwamnan na rokon Wike kada ya yi watsi da shi idan ya dawo jam’iyya mai mulki.
Rade-radin komawar Wike jam’iyyar APC sun kara karfi ne bayan Shugaba Tinubu ya mika sunansa a jerin ministocinsa.

Shugabannin PDP dai sun bayyana rashin jin dadinsu, tare da kurarin daukar mataki a kan tsohon gwamnan na Ribas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here