Ce-ce-kucen da soke lasisin makarantu masu zaman kansu ya haifar a Kano

0
268
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana soke lasisin makarantu masu zaman kansu ne ta sanarwar da mashawarcin gwamna Baba Umar ya fitar.

Sanarwar na dauke da ku-kumce makarantun masu zaman kamsu ta yadda cin gajiyar hada-hadar littafai da yunifom ya haramta garesu.

Baba Umar ya shaidawa manema labarai cewa ” zan yi aikina tsakani da Allah zan taimaki iyayen yara wajan ganin an daina zaluntarsu ta hanyar cunkusa musu abuwan rashin ka’ida ta fuskar kayan makaranta da sauran abubuwan da suka shafi karatun ‘ya’yansu, sannan suma ina shawartarsu akan suke bayar da kudin makarantun nan domin kudi ake sakawa ana samar da su, sannan satifiket mun sani ana bayar da na bogi, amma nan ba da jimawa ba insha Allah za a ji tsarin da gwamnati ta tsara domin a ci gaba da gabatar da karatu cikin tsari”

Sai dai masu irin wadannan makarantu sun ce wannan mataki na gwamnati bai wuce shigar musu hanci da kudundune ba kan hana su kara kudin makaranta duba da irin wannan zamani da ake ciki na tsananin rayuwa.

Alhaji Muhammad Magaji Mahmud shine sakataren kungiyar makarantun kuma mamallakin makarantar Nyfolk da ke nan garin Kano.

Sakataren kungiyar makarantun ya ce ” gaskiya bamu ji dadin wannan hukuncin da gwamantai ta dauka ba domin bamu da wata hanya da muke samun kudi face wannan hanyar da muke karbar kudi daga hannun iyayen yara, banda haka kuma mun tsinci kan a cikin wannan tsadar rayuwa ga hauhawar farashi sannan ga tsadar abun hawa ka haraji daban-daban da muke samu ta fuskar gwamnati a karshe dai mun addu’a da kuma fatan gwamnati za ta kalli wannan al’amari da idon basira domin muma ‘ya’yanta ne kuma ‘yan jihar Kano masu neman halaliyarsu kamar yadda kowa yake fita yaje ya yi nasa kasuwancin”.

Sai dai kuma wannan lamari da ya faru iyayen yara na nuna farin ciki da hakan bisa matsin da suke fuskanta wajan bani-bani da yara ke musu na dawainiyar makarantun.

Alhaji Abdullahi guda daga cikin iyayen yana cewa ” a matsayin mu na iyaye mukan fuskanci matsaloli fiye da yadda kake tunani misali duk abunda za ka saya a Naira 10 in makaranta mai zaman kanta ne sai ka saya Naira 20 ko 15 hakan nan yunifom duba da za ka biya kudin makaranta da sauran abubuwa na rayuwa”

Ko menene matakin shari’a a kan wanna lamari?

Barrista Abdul Fagge kwararren lauya yace ” wannan mataki da gwamnati ta dauka daidai ne yana kan tsari yan kan ka’ida domin hakkinta ne ta samar da daidaito akan harkar karatun yayanta koda kuwa a kan makarantu masu zamn kansu ne”

Zama da makarantun kudi ya zama dole duba da yanda makarantun gwamnati suka zam filin allan baku babu kayan karatu babu abun zama babu muhallin karatu mai kyau ga rashin kwarewa da cancantar dayawa daga cikin malaman wanda hakan ne ya jawo iyaye ke kyamatar kai yayansu makarantun gwamnati sannan hakanne ya sanya masu makarantun kudi suka yanka suka ga jini sai suke ta wasa wukakyensu domin zubar jini mai yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here