Google zai bai wa matasa ‘yan Najeriya horo kan fasahar intanet

0
200

Google zai bai wa mata da matasa ‘yan Najeriya 20,000 horo kan fasahar intanet sannan ya bai wa gwamnatin kasar tallafin naira biliyan 1.2 don samar da ayyukan yi miliyan daya, a cewar babban jami’in kamfanin na Afirka.

Mr Olumide Balogun ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kai wa mataimakin shugaban Nijeriya Kashm Shettima a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata.

Shettima ya ce Najeriya na shirin samar da miliyoyin ayyukan yi a fannin fasahar sadarwa da harkokin kasuwanci na intanet ga mata da matasa ‘yan Nijeriya. Ko da yake bai fadi lokacin da yake sa rai samar da ayyukan ba.
Babban jami’in Google Africa ya ce za su bayar da horo da tallafin kudin tare da hadin gwiwa da kamfanonin fasaha na Data Science Nigeria da the Creative Industry Initiative for Africa.

Mr Balogun ya ce kamfaninsu zai mayar da hankali wurin taimaka wa masu kananan kamfanonin kirkira da fasahar intanet, wadanda ake kira startups ta yadda za su samar da ayyukan yi masu dimbin yawa ga ‘yan kasar.

Shettima ya ce tsare-tsaren Google sun yi daidai da shirin gwamnatin Najeriya na samun karuwar matasa a fannonin tattalin arzikin intanet.

Ya kara da cewa gwamnatinsu tana hada gwiwa da bankuna don cimma wadannan manufofi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here