Yadda farmakin  ‘yan bindiga ga sojoji ya kasance a Neja

0
265

Yan bindigan sun yi kwantan bauna ne domin dakun zuwan sojojin saboda su farmakesu wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayuwar sojoji 26 tare da raunata wasuda dama.

Bugu da kari, wani kakakin sojin sama ya sanar da cewa wani jirgi mai saukar ungulu  ya kai dauki ga wadanda suka samu rauni sai shima ya fado a ranar Litinin a yankin da dakarun sojojin ke yakar  ‘yan bindigaan, sai dai bai bayyana yaya na cikin jirgin suka kare ba.

Hafsoshin sojin biyu da suka nemi a sakaya sunayensu sakamakon rashin izinin ganawa da manema labarai, sun ce sojoji 23 ne suka mutu tare da mayakan sa-kai uku, sakamakon mummunan bata-kashi da aka yi a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina.

Wata majiyar kuma ta ce yan bindigan sun yi asarar dakarunsu da dama sama da yaya jami’an sojin suka yi.

Ta kuma ce jirgi mai saukar ungulun da ya fadi yana dauke da gwawarwakin dakaru 11 da suka rasa rayukan su da kuma wadan suka samu munanan raunuka, sanadin kuma da ya jawo faduwar jirgin shine da yan bindigan suka bude masa wuta.

A wata sanarwa, wani kakakin rundunar sojin sama, Edward Gwabket ya tabbatar da faduwar jirgin, inda ya ce ya kwashi dakarun da lamarin ya rutsa da su ne daga makarantar firamare ta Zungeru, amma ya rikito a kauyen Chukuba na karamar hukumar Shiroro a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Jihar nan ita ma ta shafe shekaru masu tarin yawa tana fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke kashe-kashe da  sace-sacen mutane don karbar kudin fansa, tare da kone-konen gidaje al’umma da kuma sace-sacen kadarorin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here