DSS ta gargadi ‘yan bindiga kan sake kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna hari

0
230

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar da sanarwar tsaro da ke kunshe da gargadi kan wani gagarumin shiri da ‘yan bindiga ke yi na sake kai harin ta’addanci wa jirgin kasan da ke zirga-zirga daga Abuja zuwa Kaduna.

Manema labarai sun rawaito cewa, an taba kai wa jirgin hari a Kaduna a kauyen Katari a ranar Litinin, 28 ga Maris, 2022, lamarin da ya sa hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da sufuri akan layin dogon.

A wata wasikar sirri mai dauke da sa hannun Daraktan DSS na rundunar FCT, R.N. Adepemu, mai taken, ‘Rahoton Tsaro: Barazana game da gamayyar Kungiyoyin ‘Yan Bindiga da ke yi na kai hari kan Jirgin Kasa da ke taso wa daga Abuja Zuwa Kaduna’, Hukumar DSS tana gargadin fasinjojin jirgin da su yi taka tsantsan.

Wata takardar sirrin ta bayyana cewa gamayyar kungiyoyin ‘yan bindiga na shirin kai hari wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da nufin yin garkuwa da fasinjojin da ke cikin jirgin domin neman kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here