Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi gargadin “mummunan sakamako” idan gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kyale lafiyar hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ta kara ta’azzara yayin da ake yi masa daurin talala kamar yadda wata sanarwa da wani jami’in Turai ya fitar a ranar Juma’a.
A yayin wani kira ga shugaban Tarayyar Turai Charles Michel, shugaban Najeriya, Tinubu kuma shugaban kungiyar ECOWAS da ke adawa da juyin mulkin Nijar ya bayyana damuwarsa game da “tabarbarewar yanayin tsare shugaba Bazoum”.
A ranar 26 ga watan Yuli ne jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka tsare tsohon shugaban mai shekaru 63 , wanda ke zaman juyin mulki karo na biyar a Nijar tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.
Tinubu ya jaddada kudirin ECOWAS da kuma manufofin siyasa na daukar mataki daya. Duk da tasirin tattalin arzikin da wasu kasashen yankin ke fama da shi, ECOWAS za ta ci gaba da tabbatar da takunkumin, kamar yadda jami’in ya tabbatar.
Charles Michel ya jaddada cewa Tarayyar Turai za ta bai wa kungiyar ta ECOWAS cikakken goyon baya ba tare da kakkautawa ba, ya kuma yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma ce Tarayyar Turai ta Æ™i amincewa da hukumomin da suka biyo bayan juyin mulkin tare da tabbatar da cewa shugaba Bazoum, wanda aka zaba bisa ka’ida, shi ne halastaccen shugaban kasar Nijar.