Tinubu ya kafa shirin bunkasa amfani da iskar gas ta CNG a motoci

0
156

A wani yunkurin gwamnatin Najeriya na bunkasa amfani da gas, nau’in CNG a matsayin makamashin da motoci ke amfani da shi, Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani shirin gwamnatin tarayya don cimma wannan manufa.

Wannan shiri wani mataki ne don rage radadin janye tallafin mai, ta hanyar rage farashin makamashi.

Manufar shirin sauya fasalin sufuri a kasar, da samar da motoci 11,500 masu amfani da CNG, da kayayyakin sauya injinan mota 55,000 daga fetur zuwa CNG.

A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, burin shirin shi ne yawaita amfani da gas din CNG a fadin Nijeriya a matsayin makamashin da motoci ke amfani da shi.

Haka nan shirin zai tallafa wa kamfanonin kere-kere da na hada kaya, su fadada yawan ma’aikatan da suke dauka, wanda shirin zai dace da muradun gwamnatin tarayya.


Abubuwan da shirin ya kunsa sun hada da horarwa, da hada kayayyakin ayyukan gas, wanda a farko zai fuskanci harkar sufurin jama’a da na dalibai, don rage kudin motacin haya ga jama’a.


Wadanda suke da hannu a shirin sun hada da kamfanonin sufuri tsakanin jihohi masu amfani da iskar gas ta CNG. Za a tallafa wa jihohi su samar da motocin bas-bas masu amfani da CNG.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here