Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan mutuwar sojojin ƙasar da aka kashe a wani ƙwanton-ɓauna da ‘yan bindiga suka yi musu tare da faɗuwar wani jirgin helikofta na soji a jihar Neja.
Cikin wani saƙon Twitter da tsohon shugaban ƙasar ya wallafa ya ce ya kaɗu da hatsarin jirgin helikoftan, bayan da kuma aka yi wa waso sojojin ƙaar kwanton-ɓauna.
“Ina miƙa soƙon jaje ga iyalan mamatan. ina kuma yi wa waɗanda suka jikkata addaua’r fatan samun lafiya”.
Buhari ya kuma aike da saƙon ta’aziyyarsa ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da rundunar sojin ƙasar.
A ranar Alhamis ne shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta 36 a wani ƙwanton-ɓauna da aka yi musu a yankin Zungeru na jihar Neja, da faɗuwar jirgin helikofta da ya ƙwaso gawarwakin sojojin da marasa lafiyar ranar Litinin da ta gabata.