Hotuna: Yadda ‘yan Nijar mazauna Kano suka yi zanga-zangar nuna goyon baya ga ECOWAS

0
173

Wasu masu zanga-zanga sun hau kan titin Wapa da ke karamar hukumar Fagge a jihar Kano da ke arewacin Najeriya suna nuna goyon bayan kungiyar ECOWAS.

Sun tattaru ne domin yin Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar tun watan Yuli da ya gabata.

Mafi akasarin masu zanga-zangar matane kuma sun taru ne a kan shatale-talen Wapa da ke cikin birnin Kano a yau Asabar suna neman sojoji su saki Shubaga Bazoum.

Hukumar tsaro na jihar Kano kuma na yi wa masu zanga-zangar barazana saboda karya dokar da masu zanga-zangar suka yi na kin neman izinin yin zanga-zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here