Zulum ya bai wa sojojin da suka jikkata a Borno N10m

0
154

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga sojojin da suka jikkata sakamakon yaƙi da Boko Haram da suke yi a jihar.

Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa shafinsa na X da a baya aka fi sani da Twitter, ya ce tallafin na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka, wata biyu da suka gabata a lokacin da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya kai ziyara jihar.

Babban hafsan sojin ƙasan dai ya je jihar ne domin gudanar da bukukuwan babbar sallar tare da dakarun ƙasar da ke fagen daga a jihar ta Bornon.

Kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida Farfesa Usman A Tar tare da babban sakataren gidan gwamnatin jihar Barrister Mustapha Ali Busuguma ne suka miƙa kuɗin ga babban kwamandan runduna ta bakwai da ke Maiduguri, Manjo Janar Peter Malla ranar Asabar.

Sojojin Najeriya da dama ne suka mutu a rikicin Boko Haram da aka ƙwashe fiye da shekara 10 ana yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihohin Borno da Yobe da wasu yankunan jihar Adamawa.

Lamarin da yayin sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da raba miliyoyi da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here