Gwaman Kaduna ya rage kuɗin makaranta a manyan makarantun jihar

0
160
Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin rage irin wahalhalun da tsadar kuɗin makaranta ke haifarwa ga al’ummar jihar.

Sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari na kuɗin makaranta da ɗalibai ke biya a jami’ar jihar Kaduna, wato KASU.

Haka nan an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.

Bugu da ƙari sanarwar ta ce an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a Kwalejin ilimi ta jihar da ke Gidan Waya.

Yayin da aka yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai masu karatun babban difiloma ke biya a Kwalejin koyar da harkokin lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi, inda su ma masu karatun difiloma za su samu ragin kashi talatin cikin ɗari.

A ƙarshe sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin koyon jinya ta jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here