Trump zai mika wuya kan zargin sauya sakamakon zabe a Georgia

0
159
Donald Trump
Donald Trump

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai mika wuya ga mahukunta a jihar Georgia a ranar Alhamis don fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa a kan yunkurin jirkita sakamakon zaben shugaban kasa na jihar da ya nuna cewa ya sha kaye a shekarar 2020.


Jim kadan bayan da alkalin kotu a Georgia ya sanar da belinsa a kan kudi dalar Amurka dubu 200, Trump ya wallafa wani sako a shafin dandalin sadarwarsa cewa, za shi Atlanta da ke Georgia don mika wuya ga jami’an tsaro su kama shi.

Wannan zai kasance karo na 4 da ake kama Trump tun a watan Afrilu a lokacin da ya kasance shugaban Amurka na farko da aka tuhuma da aikata laifi a hukumance a tarihin kasar.

Tun bayan wannan lokaci, Trump, wanda ya ci gaba da zama a kan gaba daga cikin masu takarar shugabancin kasar a jam’iyyar Republican, ya yi ta fuskantar kiraye-kiraye da sammace-sammace a kotunan kasar.

Sanarwar Trump ta zo ne sa’o’i bayan da masu taimaka wa alkalai da masu gabatar da kara suka gana don tattauna batun bada belinsa.

Bisa yarjejeniyar belinsa, an haramta wa tsohon shugaban aikata duk wani abin da zai kasance tamkar barazana ga wadanda ake tuhumar su tare, shaidu da ma wadanda abin da ya aikata ya shafa, kamar yadda takardar yarjejeniyar belinsa din da alkalin lardin ,Fulton Fani Willis ya sanya wa hannu ta nuna.

Wannan tuhuma ta Georgia ta zo ne makwanni biyu bayan da babban lauyan Ma’aikatar Shari’ar Kasar ya tuhumi Trump a kan abin da ya shafi hadin baki don sauya sakamakon zaben da ke nuna ya sha kaye. Baya ga wadannan tuhume-tuhume biyu masu nasaba da juna, Trump na fuskantar tuhumar hadin baki wajen boye kundaye da suka kunshi bayanan sirri da suka shafi kasar da kuma tuhumar da ake masa a birnin New York a game da gabatar da bayanan bogi a game da kasuwancinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here