Daliban Kuriga: Ba za mu biya kudi ga yan ta’adda ba – Tinubu

1
134

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake jaddada umarninsa ga jami’an taron ƙasar da su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da ɗaliban makarantar Kuriga da ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata.

Cikin wani jawabi da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya yi wa manema labarai, jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar da aka gudanar a fadar gwamnati, ministan ya ce gwamnati ba za ta biya ko sisin kobo ba a matsayin fansa ga maharan don sakin ɗaliban.

Ministan ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta lamunci ci gaba da sace ɗalibai don yin garkuwa da su ba, don haka ya ce gwamnati ke kira ga jami’an tsaron da su yi duk abin da ya kamata don tabbatar da sakin ɗaliban da sauran mutanen da hannun ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.

”Idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da ƙarfin tuwo wajen kuɓutar da ɗaliban nan, saboda hukumomin tsaronmu a shirye suke ko me za a yi a dawo da waɗanna ɗaliban”, in ji shi.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar furamare da ƙaramar makarantar sakandiren Kuriga, inda suka sace ɗalibai fiye da 280, kodayake gwamnan jihar Uba sani ya ce daga baya wasu 28 sun kuɓuta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here