Vladimir Putin ya sake samun karin wa’adin zama a karagar mulkin Rasha na karin shekaru 6 kamar yadda sakamakon zaben kasar ya nuna a ranar Lahadi, lamarin da ya sa shugaban, wanda tsohon jami’in leken asiri ne zai kasance wanda ya fi dadewa a kan karagar mulkin kasar a cikin shekaru 200.
Sakamakon da aka tattara a yayin da masu zabe ke barín rumfunan kada kuri’a ya nuna cewa Putin ya samu nasarar lashe kashi 87 cikin dari na kuri’un da aka kada bayan da aka rufe rumfunan zabe a yankin Kaliningrad na yammacin kasar.
Fadar gwamnatin Rasha ta bayyana wannan zabe a matsayin wata dama da ‘al’ummar kasar za su yi amfani da ita wajen bayyana goyon bayansu ga matakin sojin da take dauka a kan Ukraine, inda ma har aka kada kuri’a a yankunan UKraine da ke karkashin ikon Rasha.
A jawabin da ya gabatar a wani taron manema labarai a wannan Litinin, bayan wannan sakamako, Putin mai shekaru 71 ya ce Rasha ba za ta mika wuya ga duk wata barazana ba, a yayin da yake jinjina wa al’ummar kasar da suka ba shi karin wa’adi musamman ma dakarun Rasha da ke fagen daga a Ukraine.
A waje daya kuma, Ukraine da kawayenta sun caccaki wannan sakamako, su na mai bayyana saben a matsayin na jeka-na-yi-ka, a yayin da shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana Putin a matsayin dan kama-karya, wanda giyar mulki ke tasiri a kansa.
Idan Putin ya kammala wannan wa’adi, zai kasance shugaban Rasha mafi dadewa a kan karagar mulki tun bayan Catherine the Great a karni na 18.